Mahukuntan Najeriya sun kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba na tattaunawa da jagororin kungiyar Boko Haram na hakika, ta yadda su kuma za su saki 'yan mata sakandaren Chibok da suke rike da su tun a shekarar 2014.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a birnin Legas. Yana mai cewa, tun ba yau ba gwamnatinsa ta bayyana kudurinta na tattaunawa da jagororin kungiyar da suka san inda ake tsare da wadannan 'yan mata.
Buhari ya kuma baiwa shugabannin kungiyar Boko Haram din zabin cewa, idan har ba sa son tattaunawa da su kai tsaye, to, suna iya zabar wata fitacciyar kungiyar kasa da kasa mai zaman kanta don a tattauna da su a madadinsu.
Sai dai kuma shugaba Buhari ya yi gargadin cewa, gwamnati ba za ta bata lokaci da kundinta wajen tattaunawa da kafofin da ake da shakku kansu wadanda ke ikirarin cewa, sun san inda wadannan 'yan mata suke ba.
Shugaba Buhari ya ce, yanzu haka sojojin kasar tare da taimakon takwarorinsu na kasashen Chadi, Kamaru, Nijar da kuma Benin sun karya lagon kungiyar wadda a baya ta yi mubaya'a da kungiyar ISIS.(Ibrahim)