in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin 'yan Najeriya ya karu zuwa miliyan 182
2016-11-11 09:33:59 cri

Mahukunta a Najeriya sun bayyana cewa, yawan al'ummar kasar ya karu zuwa mutane miliyan 182, kuma sama da rabin jama'ar kasar 'yan kasa da shekaru 30 ne.

Ghaji Bello shi ne shugaban hukumar kidayar yawan mutane ta Najeriya, ya ce an gano adadin yawan jama'ar kasar ne ta hanyar alkaluman kididdiga daga adadin mutane miliyan 140 da aka samu a kidayar jama'a da aka gudanar a kasar shekaru 10 da suka gabata, inda aka samu karuwar jama'a da kashi 3.5 cikin dari, bayan yin la'akari da karuwar alkaluman kididdiga na tsawon shekarun al'umma, da kuma raguwar yawan mutuwar kananan yara a kasar.

A cewar wani rahoto da jaridar Vanguard ta kasar ta fitar, ta ce akwai yiwuwar za'a gudanar da aikin kidayar jama'a a wannan shekara, domin tantance yawan jama'ar kasar na baya bayan nan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China