in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta mai da hankali kan kasashen Afrika don bunkasa fitar da kayayyakinta
2016-11-10 09:53:42 cri

Kasar kenya ta fara wani shiri da zai mai da hankali wajen karfafa dangantakarta da kasashen nahiyar Afrika domin bunkasa harkokin cinikayya. Daraktan hukumar raya fitar da kayayyaki zuwa ketare ta kasar Solomon Boit, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Nairobi. Boit ya bayyana a lokacin bude bikin baje koli karo na 34 a kasar Indiya cewa, Kenya ta yi nazari kan wasu kasashe na Afrika da suka hada da demokaradiyyar Congo, Habasha, Najeriya, Rwanda, Angola, wadanda suke da manyan kasuwannin sayar da kayayyakin kasar Kenya.

Ya ce, sun lura cewa, akwai gagarumar kasuwa a Afrika ta irin kayayyakin da kasar Kenyan ke samarwa, wadda za ta ba da dama ga kasar wajen bunkasa fitar da kayayyakinta zuwa kasashen ketare.

Ya kara da cewa, nasarar da kasashen Afirka suka samu wajen karuwar tattalin arziki a shekaru 10 da suka gabata, ta bai wa kasar ta Kenya dama wajen sayar da kayayyakinta a kasuwar Afirka.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China