Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya soke wata ziyarar aikin da zai kai a kasar Angola bisa dalilin wani kazamin harin ta'addanci da aka kai a wani otel dake wani birnin kasar Kenya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 12 a ranar Talata.
Kakakin fadar shugaban kasa, Manoah Esipisu, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, shugaba Kenyatta ya soke wannan ziyara don halartar wani taro kan tsaro domin kawo goyon baya ga iyalan da suka rasa 'yan uwa da kuma mutanen da suka jikkata, wadanda muke fatan su sami sauki cikin gaggawa.
Kungiyar Al-Shabaab, dake kasar Somaliya, ta dauki alhakin kai wannan hari a otel din dake birnin bakin ruwa na Mandera a ranar Talata da safe.
Shugaban Kenya ya yi allawadai da babbar murya da wannan kazamin hari da wasu mutane maras imani suka kai, in ji wannan sanarwa.
Da farko a cikin wannan wata, wani harin ta'addanci kan yankin mazauna a Mandera, birnin mai iyaka da Somaliya, ya yi haddasa mutuwar mutane 6. Mayakan sun kai harin nasu a kan wadanda ba musulmai ba a yayin wadannan hare hare biyu.
Lamarin ya rutsa da namiji goma sha daya da mace guda, in ji mista Saleh, tare da bayyana cewa, har yanzu ba'a tantance gawawwakinsu ba.
Maharan sun yi amfani da nakiyoyi masu fashe da aka hada da hannu domin tarwatsa wani bangaren otel din a yayin wannan hari. (Maman Ada)