Kasar Kenya na hasashen bude wata cibiyar kudin kasa da kasa ta Nairobi (NIFC) a farkon shekarar 2017, domin mayar da babban birnin kasar wata cibiyar hada hadar kudi ta shiyyar, in ji wani babban jami'in Kenya a ranar Talata.
Darekta janar game da harkokin tattalin arziki da kasafin kudin kasa a baitulmali, Geoffrey Mwau, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai a Nairobi cewa, Kenya tuni ta tsara wani tsarin shari'a da doka domin wannan NIFC.
Da zaran an kafa NIFC, za ta taimaka ga tattara hankalin gamayyar kudin kasa da kasa zuwa yankin gabashin Afrika, in ji mista Mwau a albarkacin kaddamar da dandalin kasa da kasa kan kananan bankuna na muslunci.
Wannan taro na kwanaki biyu da ya hada wakilai wajen dari guda domin yin nazari kan hanyoyin bunkasa bangaren kudin shiyya da wata cibiyar kudi a Kenya, in ji mista Mwau.
NIFC na daya daga cikin muhimman ayyuka biyu na bangaren kudi a kasar Kenya, gudan kuma shi ne na bunkasa da aiwatar da wani babban shirin kasuwar hannayen jari.
A cewar ma'aikatar baitulmalin kasa, wadannan mahimman ayyuka ba za su samu nasara ba sai idan Kenya ta iya samun moriya daga damammakin da bankunan muslunci suke bayar.
Bankunan musulunci na samar da manyan damammaki ba ma a sauran sassan fadin duniya ba, har ma a kasar Kenya, in ji mista Mwau. (Maman Ada)