in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin kasashen Afirka sun alkawarta tallafawa Kenya a fannin yawon shakatawa
2015-05-13 10:40:28 cri

Wasu ministocin kasashen Afirka sun bayyana aniyarsu ta tallafawa kasar Kenya wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa, harkar da ta yi matukar samun koma baya, sakamakon matsalolin tsaro dake addabar kasar.

Wata sanarwa da hukumar kula da harkokin yawon shakatawar kasar ta fitar, ta ce, ministocin sun bayyana wannan kuduri ne yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Talatar makon jiya a kasar Afirka ta Kudu.

Mahalarta taron sun ce, daukar wannan mataki ya zama wajibi, duba da kasancewar yawon shakatawa fanni na biyu, wajen samarwa Kenyan kudaden shiga.

Da yake karin haske game da hakan, ministan harkokin yawon shakatawa na kasar Afirka ta Kudu Derek Hanekom, ya ce, taron mai lakabin "INDABA", wanda ake gudanarwa a Afirka ta Kudu a cikin wannan wata na Mayu, shi ne taro mafi girma da ya shafi harkokin yawon shakatawa a Afirka.

Mr. Hanekom ya kara da yin kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a fannin da su tallafawa Kenya, wajen magance matsalolin tsaro wadanda ke da nasaba da sauran kasashen dake nahiyar.

A nasa bangare, daraktan hukumar MDD mai kula da harkokin yawon shakatawa a Afirka Elcia Grandcourt, jan hankalin kasashen Afirka ya yi, game da muhimmancin hadin gwiwar su a fannin bunkasa wannan sashe, ta yadda nahiyar za ta ci karin gajiya daga harkokin yawon shakatawa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China