Kalubalolin ci gaba mai karko a Afrika da yaki da ta'addanci sun kasance manyan batutuwa na ayyukan zaman taron shugabannin majalisun dokoki na kungiyar 'yan majalisun Afrika (UPA) karo na 39 da aka bude a ranar Talata a cibiyar zauren masharwata wato zaure na biyu na majalisar dokokin Morocco dake birnin Rabat.
Mahalarta a wannan haduwa za su mai da hankali kan halartar 'yan kasa, musammun ma matasa kan bunkasa tsarin demokaradiya da yaki da ta'addanci a Afrika, in ji Abdelhakim Benchamach, shugaban zauren mashawarta a gaban 'yan jarida.
Haka zalika, mahalartan za su tattauna rawar da 'yan majalisun dokokin Afrika za su taka wajen tabbatar da muradun ci gaba mai dorewa, ta yadda za a fadada muryar Afrika game da wannan batu, da kuma fitar da wani tsinkaye na hadin gwiwa kan wannan batu, da ya kamata a gabatar a yayin taron COP22 a Marrakech, in ji mista Benchamach. (Maman Ada)