in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Afrika sun yi alkawarin karfafa matakan yaki da ta'addanci
2014-09-03 10:32:39 cri

Shugabannin nahiyar Afrika, da suka yi taro a ranar Talata a birnin Nairobi bisa tsarin dandalin kungiyar tarayyar Afrika (AU) kan wanzar da zaman lafiya da tsaro, sun yi alkawarin kara karfafa matakan yaki da ta'addanci da kaifin akidunsa dake kasancewa wata sabuwar barazana ga zaman karko da cigaban nahiyar.

Shugabannin sun jaddada cewa, amsa guda cikin hadin gwiwa ita ce muhimmiyar hanyar samun galaba kan ta'addanci da munanan tashe-tashen hankali.

Kungiyoyin ta'addanci a nahiyar Afrika sun samu cigaba ta fuskar kwarewa da gudanar da munanan ayyukansu. Ya kamata mu kara karfafa matakan da za su taimaka wajen kawo karshen wannan bala'in, in ji shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta a gaban takwarorinsa na Tanzaniya, Uganda, Somaliya, Nijeriya da Chadi.

Mista Kenyatta ya nuna cewa, Afrika na cikin barazanar ta'addanci dalilin rashin ingancin iyakokinta, talauci da rashin aikin yi ga matasa. Haka kuma ya ba da shawarar bullo da sabbin matakai, kamar kafa wata gidauniyar yaki da ta'addanci domin kara azama wajen yaki da wannan barazana.

A nasa bangare, shugaban kasar Chadi Idris Deby ya bayyana cewa, ya kamata gwamnatocin Afrika su mai da hankali sosai kan ta'addanci da yadda ake yada akidun kaifin kishin islama.

Yayin da shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi kira ga gwamnatocin Afrika da su yi kokarin warware duk wasu rikice-rikicen dake nasaba da barkewar ta'addanci, misalin rikicin kabilu, rashin aikin yi ga matasa, da rashin mulki na gari. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China