in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen yammacin Afirka na karfafa matakan dakile hanyar samun kudin ta'addanci
2015-10-15 10:39:04 cri

Kwararrun kasashe masu amfani da harshen Faransanci dake yammacin Afrika sun kaddamar tun a ranar Talata, a birnin Lome, da aiwatar da kudurin kwamitin tsaro na MDD dake shafar karfafa matakan yaki da hanyoyin samun kudin ta'addanci.

Wannan taron kara wa juna sani na kwanaki uku da gungun kasa da kasa na yaki da halatta kudin haram a yammacin Afrika (GIABA) ya shirya na da manufar taimakawa kasashe mambobin wannan kungiya kafa wasu matakan sanya takunkumi ta fuskar kudi ga wadanda ake tuhuma.

Aiwatar da wadannan matakan sanya takumkumi da aka tsai da, za'a yi shi daidai da tanade tanaden kudurorin kwamitin tsaro na MDD dake da nasaba da yin rigakafi da kuma yaki da ta'addanci da hanyoyin samun kudinsa, in ji masu shirya wannan zaman taro.

Haduwar ta Lome na duba matsayin aiwatarwa, tsare tsaren da suka dace, aiwatarwa mafi kyau ta dabaru da suka dace, ta yadda za a aiwatar da tantance hanyar da doka ta tanada wajen rike kudin mutane ko kungiyoyin da ake zargi dake cikin bankuna.

A gaban wadannan hanyoyin samun kudin ta'addanci, dole a samu wani tsari na shari'a, domin samun karfin gurfanar da ta'addanci, in ji Babacar N'Diaye, darektan zartaswa da kudi na kungiyar GIABA. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China