in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saliyo ta yi bikin murnar cika shekara daya ta ban kwana da cutar Ebola
2016-11-09 10:42:51 cri

Al'ummar kasar Saliyo sun yi bikin murnar ban kwana da cutar Ebola, tun bayan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana kasar a matsayin wacce ta yi nasarar kawar da cutar ta Ebola daga kasar shekara guda.

Domin munar wannan rana, jama'ar kasar ta Saliyo sun yi shigar kaya mai launin ruwan dorawa tun da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Litinin, al'ummar kasar sun yi shiru na tsawon mintoci 3, domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyyar cutar Ebola.

A jawabin da ya gabatar ga al'ummar kasar da misalin karfe 11 da mintuna 3, shugaban kasar Ernest Bai Koroma, ya ce, al'ummar kasar Saliyo sun fara aiki babu kakkautawa domin farfadowa daga ibtila'in da kasar da fuskanta tun bayan bullar cutar ta Ebola mai saurin hallaka jama'a, shugaban ya yi tsokaci game da irin ta'annati da cutar ta yi ga rayuwar jama'a, da koma bayan tattalin arziki da kasar ta fuskanta.

Ya kara da cewa, mutane dubu 8 ne suka kamu da cutar a fadin kasar, kuma daga cikinsu mutane 3,589 sun rasa rayukansu, ciki har da ma'aikatan lafiya 221.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China