Kasar Saliyo, daya daga cikin kasashen yammacin Afrika da annobar cutar Ebola ta fi shafa a shekarar da a gabata, ta kaddamar da wani aikin kasancewa kasar da babu cutar Ebola kwata kwata.
Shugaban kasar, Ernest Bai Koroma, ya yi jawabi a ranar Asabar a albarkacin kwanaki 21 na farko da ba a samu cutar Ebola ba.
Wannan wani muhimmin mataki ne na farko a cikin yakin da kasar take yi da Ebola, kuma babu shakka za a cimma nasara, in ji mista Koroma.
Ya dauki mutane kusan dubu hudu da suka tsira daga cutar Eboka a kasar a matsayin jarumai, tare da yin kira ga al'ummar kasa da kada su nuna dari dari da wadannan mutane.
Dukkan 'yan Saliyo ya kamata su kasance masu alfahari da abin da muka cimma, mu kawar da tsoro, in ji shugaban Saliyo.
Haka kuma mista Koroma ya bayyana cewa, muna yaki da cutar Ebola tare, za mu samu nasara tare, kuma ba za mu ja da baya ba.
A cewar hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, wata kasa ba za ta iya cewa babu Ebola kwata kwata ba, sai bayan kwanaki 42 daga mutum na karshe da ya kamu, abin da ke nufin cewa, ranar 8 ga watan Nuwamba za ta kasance ranar Saliyo, idan har ba a gano wani mutum mai dauke da Ebola ba, to za a bayyana cewa, babu cutar Ebola a kasar baki daya.
Domin kare mutane daga kamuwa, wasu masanan kasar Sin sun bullo da wata allurar da a yanzu haka ake gwajinta a Saliyo a matsayin mataki na biyu na gwajin, bayan an kammala mataki na farko a kasar Sin.
Allurar tana nuna kyau da inganci, ba ta da illoli sosai, kuma ba a samu yawan korafe korafe ba kan wannan allura, in ji wata sanarwar ma'aikatar kiwon lafiya ta Saliyo.
Yan Saliyo fiye da 100 masu shekaru 18 da 50 da aifuwa suna cikin koshin lafiya da suka amince da a yi gwajin wannan allura kansu. (Maman Ada)