in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya yi allahwadai da kisan ma'aitakan wanzar da zaman lafiya a DRC
2015-05-07 10:13:24 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya yi kakkausar suka kan yadda aka halaka wasu ma'aikatan da ke aikin wanzar da lafiya guda biyu 'yan kasar Tanzaniya a gabashin Jamhuriyar Demokiradiyar Congo DRC.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq wanda ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ya kuma ce, harin na ranar Talata da aka kai a yankin Beni ya yi sanadiyar jikkatar wasu ma'aikatan 13, baya ga wasu karin ma'aikatan da ka ba da rahoton bacewarsu. Ko da ya ke daga bisani an gano inda suke.

Mambobin kwamitin sulhun sun kuma aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, gwamnati, al'ummar Tanzaniya da kuma MONUSCO, sannan suka yi fatan wadanda suka jikkata za su warke cikin hanzari.

Bugu da kari kwamitin sulhun ya yi kira ga gwamnatin Jamhuriyar Demokiradiyar Congo da ta hanzarta gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki, tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Daga karshen kwamitin sulhun ya bayyana cewa, hare-haren da ake kaiwa ma'aikatan wanzar da zaman lafiya tamkar aikata laifufukan yaki ne karkashin dokokin kasa da kasa. Kuma hakan ba zai sanya gwiwarsu na ci gaba da baiwa wakilin musamman na babban sakataren MDD da ke DRC da MONUSCO goyon bayan sauke nauyin da aka dora musu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China