in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da a dauki matakan warware sabanin siyasa a DRC
2015-01-23 09:36:33 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a rikicin siyasar jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC, da su kai zuciya nesa, su kuma gaggauta fara gudanar da shawarwari.

A cewar kakakin MDD Stephane Dujarric, Ban Ki-moon na da burin ganin an gudanar da shawarwari kan batutuwan da suka shafi babban zaben kasar, da batun wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Hakan dai na zuwa ne bayan barkewar wata tarzoma a kasar, wadda ta yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama, sakamakon shawarar aiwatar da wata doka, ta dage lokacin gudanar babban zaben kasar na badi.

Rahotanni sun bayyana cewa, burin dage zaben, ta yadda shugaba Joseph Kabila zai zarce kan karagar mulki har bayan watan Disambar shekarar mai zuwa ne ya haddasa barkewar tarzomar.

Game da yanayin da ake ciki a kasar, babban magatakardar MDD ya bukaci dakarun tsaron kasar, da masu zanga-zanga, da ma sauran al'ummar kasar da su kaucewa rura wutar rikici. Kaza lika ya bukaci mahukuntan kasar da su dauki matakan magance kazantar al'amura, ta hanyar ba da damar furta albarkacin baki, da kuma tabbatar da kare hakkokin jama'a. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China