in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya da Uganda za su samar da rundunar 'yan sandan hadin gwiwa don tabbatar da tsaro
2016-08-25 10:10:21 cri

Kasashen Kenya da Uganda sun amince su samar da rundunar 'yan sandan hadin gwiwa a tsibirin Migingo, domin samar da tsaro a kan iyakokin kasashen biyu.

Jami'in 'yan sandan Kenya Joseph Boinnet ya shedawa 'yan jaridu a birnin Nairobi cewa, za'a tura rundunar 'yan sandan hadin gwiwar zuwa tsibirin ne dake tafkin Victoria domin tabbatar da tsaro ba sani ba sabo matukar aka kama masu laifi babu sassauci ko nuna banbanci.

Boinnet ya bayyana cewa, a lokacin gudanar da sintirin hadin gwiwa, a kalla adadin 'yan sandan da kowace kasar za ta samar a dukkan kananan yankunan tsibirran ba za su zarta 12 ba.

Wannan mataki ya biyo bayan rahoton da kafafen yada labarai suka fitar ne, dake nuna cewa, mazauna yankunan tsibiran na fuskantar cin zarafi daga jami'an 'yan sanda na kasashen biyu.

Kasashen biyu sun amince su samar da rundunar 'yan sanda ta musamman wacce za ta mai da hankali a arewaci, wadda za ta hade tashar ruwan Mombasa ta kasar Kenya zuwa yankin kasar Uganda.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China