in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 14 sun mutu a harin da aka kai a wani masallaci a Najeriya
2015-10-16 09:42:04 cri

Rundunar 'yan sandan jihar Borno da ke Najeriya ta bayyana cewa, mutane a kalla 14 ne suka mutu bayan da wasu tagwayen bama-bamai suka fashe a wani masallaci a wajen Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno da ke arewa maso gabashin tarayyar Najeriya.

Kwamishian 'yan sandan jihar Borno Aderemi Opadokun ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, harin na ranar Alhamis da aka kai a masallacin da ke unguwar Molai ya kuma jikatta mutane da dama.

Aderemi ya kara da cewa, an dasa bama-baman ne a ciki da wajen masallacin, lamarin da ya yi sanadiyar rushewar masallacin baki daya.

An kuma garzaya da mutanen da suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri da sauran manyan asibitoci dake birnin na Maiduguri.

Jami'in 'yan sandan ya kuma bayyana cewa, jami'an tsaro sun iso wurin da lamarin ya faru domin killace yankin. Harin na ranar Alhamis dai shi ne na biyu cikin wannan mako da aka kai a garin na Maiduguri, babban birnin jihar Borno, bayan wasu jerin hare-haren kunar bakin wake da suka yi sanadiyar rayukan mutane 8 da aka kai a wasu sassa daban-daban na birnin.

Ana zargin mayakan Boko Haram da kai wadannan hare-hare, kungiyar da ta shafe shekaru da dama tana kaddamar da hare-hare a yankin arewacin kasar, a kokarin da take na kafa kasar musulunci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana dakarun kasar wa'adin nan da watan Disamba kan su kawo karshen ayyukan kungiyar a kasar baki daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China