in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya ba da umarnin bincike kan zargin cin zarafin 'yan gudun hijira
2016-11-01 09:24:41 cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umarnin gudanar da binciken gaggawa, game da zargin da kungiyar "Human Rights Watch" ta yi, na cewa ana cin zarafin 'yan gudun hijirar kasar dake zaune a sansanonin kula da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a jiya Litinin, ta hakaito shugaba Buhari na bayyana matukar damuwa ga rahoton na Human Rights Watch, yana mai kira ga 'yan sanda, da gwamnonin yankunan da abun ya shafa, da su binciki wannan zargi ba tare da wani bata lokaci ba. Ya ce, sakamakon binciken da aka yi ne zai ba da damar daukar mataki na gaba.

Binciken dai zai mai da hankali game da zargin lalata da mata da 'yan mata a sansanin 'yan gudun hijira. Kungiyar ta Human Rights Watch dai ta ce ta tattara bayanai da dama, game da yadda aka ci zarafin mata su kimanin 43, ta hanyar fyade da sauran hanyoyi na zalunci a sansanonin 'yan gudun hijira 7 dake birnin Maiduguri dake jihar Borno.

Mahukuntan Najeriya dai sun ce, suna daukar dukkanin matakan da suka wajaba, na baiwa 'yan gudun hijirar kariya, yayin da sojojin kasar ke ci gaba da fatattakar mayakan Boko Haram a dukkanin sassan arewa maso gabashin kasar, a wani mataki na kokarin mai da 'yan gudun hijirar zuwa garuruwan su na asali.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China