Shugaban kasar Nigeriya Muhammadu Buhari zai je kasar Kamaru bayan kammala azumin watan Ramadan don tattaunawa da takwaransa Paul Biya game da batun yaki da ta'addanci.
Kamar yadda kakakin fadar shugaban kasar Femi Adesina ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Talata, ziyarar ta zo ne sakamakon gayyatar da shugaba Biya ya aiko na bukatar su hadu a tattauna da sauran kasashe makwabta a kan yaki da ta'addanci.
Ministan mulkin yanki da daidaita kasa ta Kamaru, Sadi Rene Emmanuel ne ya kawo wa shugaba Buhari wasikar gayyatar.
Sanarwar ta ce, shugaba Buhari ya amince da halartar tattaunawar a kasar Kamaru, in an kammala azumin watan Ramadan. (Fatimah)