in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara koyar da Sinanci na karatun shekarar 2015-2016 a Benin
2015-10-12 10:34:57 cri

An yi bikin bude aikin koyar da harshen Sinanci na karatun shekarar 2015-2016 a ranar Asabar da yamma a cibiyar yada al'adun kasar Sin dake Cotonou, babban birnin tattalin arzikin kasar Benin a karkashin jagorancin hukumomin al'adu na kasashen biyu.

A yammacin ranar Asabar, mutane fiye da dari 'yan kasar Benin masu sha'awar koyon harshen Sinanci da kuma iyayensu, da ma sauran jama'a suka halarci bikin bude aikin koyar da harshen Sinanci na karatun wannan shekarar ta 2015-2016.

Bikin ya gudana tare da wani gajeren wasan kwaikwayo dake nuna wasu kananan yara masu kasa da shekaru goma sha biyu da aifuwa suna koyon harshen Sinanci, har ma da nune nunen wasannin motsa jiki na karate.

Wannan dama ta koyon harshen Sinanci da ta samu ga masu sha'awar koyo 'yan kasar Benin, za ta ba su damar kasancewa wakilai na al'adu tsakanin Sin da Benin, kuma fahimtar harshen Sinanci zai bude musu kofofin al'adun kasar Sin, in ji Bai Guangming, darektan cibiyar yada al'adun Sin dake Benin.

Dake yake jawabi a yayin wannan bikin, darektan bunkasa al'adu na ma'aikatar al'adun Benin, Patrick Idohou, ya bayyana cewa, wannan aikin koyarwa na da manufa daya, wato ita ce ta yaukaka al'adu iri daban daban tsakanin Benin da Sin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China