in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwalejin Confucius za ta fara koyar da yara marasa gata Sinanci a Benin
2015-06-04 09:25:21 cri

A wani mataki na bunkasa ayyukanta na ilmantarwa, kwalejin Confucius dake kasar Benin, ta ayyana shirinta na shigar da yaren Sinanci, cikin darussan da za a rika koyar da yaran dake kauyen SOS, na yara masu rangwamen gata.

A cewar daraktan kwalejin Dr. Julien Segbo, hakan zai baiwa yaran karin dama ta cimma burukansu na rayuwa. Ya ce, aiwatar da wannan manufa daya ne daga muhimman ayyuka da kwalejin ta tanada, cikin ayyukanta na bikin ranar yara a bana.

Kaza lika Dr. Segbo ya ce, kwalejin Confucius, ta rabawa yara kanana dake kauyen na SOS litattafai, da kayayyakin wasa, domin faranta rayukansu.

Da yake mai da jawabi game da wannan abun alheri, shugaban sashen tsare-tsare na kauyen SOS Wilfried Aime Tchibozo, ya godewa jami'an kwalejin ta Confucius, bisa wannan namijin kokari da suka gudanar, yana mai fatan za a ci gaba da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu wajen bunkasa rayuwar yara marasa gata.

Kimanin 'yan kasar Benin 3,000 ke daukar darussa daga shirye-shirye kwalejin Confucius, a matakan ilimi daban daban. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China