in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fararen hula na ci gaba da kauracewa Najeriya, in ji UNHCR
2015-07-22 10:34:40 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ko UNHCR a takaice, ta ce, 'yan Najeriya da dama na ci gaba da ficewa zuwa kasashe makwafta, sakamakon tashe-tashen hankula dake addabar arewa maso gabashin Najeriyar.

Da yake karin haske game da hakan, kakakin babban magatakardar MDD Farhan Haq, ya ce, yanzu haka 'yan Najeriyar da dama na tururuwa zuwa yankunan arewa mai nisa dake kasar Kamaru.

Ya ce, 'yan gudun hijirar na tafiya mai nisa zuwa sansanin Minawao, wanda hukumar UNHCR, da hadin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki ke daukar nauyi.

A daya hannun kuma, mahukuntan yankin Diffa dake kasar Nijar na cewa, cikin 'yan kwanakin baya bayan nan, kimanin mutane 2,500 ne suka tsallaka zuwa yankin daga Najeriya, sakamakon hare-haren da mayakan Boko Haram suke kaddamarwa, ciki hadda na garin Damassak wanda ya auku cikin makon jiya.

Mr. Haq ya ce, mafiya yawan 'yan gudun hijirar mata ne, da yara kanana da kuma tsofaffi. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China