in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar tana neman taimako domin yaki da zazzabin kwarin Rift
2016-10-27 10:12:12 cri

Gaban matsalar annobar zazzabin kwarin Rift, wadda ta kashe mutane kusan talatin tun cikin watan Agustan da ya gabata a tsakiyar kasar Nijar, hukumomin kasar sun bukaci tallafin kasa da kasa domin yaki da wannan bala'i.

Ya zuwa ranar 19 ga watan Oktoba, annobar ta janyo mutuwar mutane 30 bisa jimillar mutane 130 da suka kamu a cikin gundumomin Tassara da Tchintabaraden dake yankin jihar Tahoua dake tsakiyar kasar, a cewar wani sakamakon binciken ma'aikatar kiwon lafiyar kasar.

Domin fuskantar wannan matsala yadda ya kamata, gwamnatin Nijar tana kokarin kafa wani shirin hadin gwiwa da zai kula da kiwon lafiyar jama'a, dabbobi da muhalli a karkashin taimakon abokan huldarta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China