A ranar Talata kasashen Aljeriya da Nijer suka tattauna hanyoyin da za su kulla dangantakar yaki da ta'addanci da tabbatar da tsaro a yankunan kudu da hamadar Sahara.
Ministan harkokin wajen Nijer Ibrahim Yakubu ya fadawa 'yan jaridu cewar, bayan tattaunawa da takwaransa na Aljeriya Ramtane Lamamra, kasashen Nijer da Aljeriya sun amince za su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu domin tabbatar da tsaro a yankunan.
Babban jami'in diplomasiyyar na jamhuriyar Nijer ya tabbatar da cewar, akwai kyakkyawar mu'amala da fahimtar juna tsakanin kasashen biyu dake makwabtaka da juna, sannan ya yabawa kasar Aljeriya bisa irin kokarin da take wajen yaki da ta'addanci.
Kasar Ajriya ta girke dakaru a kudancin kasar mai tazarar kilomita 1,200 dake makwabtaka da kasashen Mali da Nijer, domin dakile aniyar bazuwar makamai da 'yan tawaye a yankunan.(Ahmad Fagam)