Tsohon ministan tsaron Najeriya Alex Badeh ya fara sabuwar rayuwa a gidan yari tun daga ranar Litinin din da ta gabata sakamakon samun sa da laifukan zambar kudaden gwamnati, da cin amanar kasa.
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa ne wato EFCC, ta damke Badeh bayan samun sa da laifuka 10 da suka shafi halasta kudin haram tun a makonni 3 da suka gabata.
Haka zalika, hukumar ta EFFC, tana tuhumar tsohon hafsan da laifin karkatar da kudin da gwamnati ta ware na sayen makamai wanda yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 19.5, a lokacin yana rike da mukamin ministan tsaron kasar.
Sai dai Badeh, bai amsa laifukan da ake tuhumarsa ba, wata babbar kotun tarayya dake Abuja, helkwatar mulkin kasar ta ki amincewa da ba da belinsa, inda ta ba da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan yari.
Tun daga lokacin da ya amshi mulkin kasar a watan Mayun shekarar 2015, shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin yaki da rashawa a kasar.
Najeriya na bin bahasin yadda aka salwantar da kudaden sayo makamai, wanda adadinsu ya zarta dalar Amurka biliyan 2.(Ahmad Fagam)