Wani babban jami'in MDD a ofishin yammacin Afrika Mohammed Ibn Chambas ya bayyana cewa, kungiyar mayakan Boko Haram ba su samu nasarar yin zagon kasa ga babban zaben Nigeriya ba, ganin yadda aka rage masu tasiri a arewa maso gabashin kasar da suka yi katutu.
Wannan bayanin ya fito ne lokacin da shugaban ofishin majalissar dake yammacin Afrika Mohammed Ibn Chambers ke bayani kai tsaye a gaban zauren kwamitin tsaro na majalissar tare da mataimakiyar shugaba mai kulawa da ayyukan ba da agajin gaggawa na majalissar Kyung-wha Kang a game da ayyukan kungiyar mayakan na Boko Haram.
Kwamitin mai mambobi 15 dai sun zauna ne musamman domin tattauna barazanar ta'addanci da zaman lafiya da kwanciyar hanakali da mayakan ke kawo wa duk duniya baki daya. Chambas ya ce, an rage karfin kungiyar kwarai duk da har yanzu suna ta aikata mummunan ta'asa. Babban magatakardar MDD dai a ranar Lahadin nan ya yaba kwarai da kokarin 'yan kasar ta Nigeriya a kan nasarar yin babban zabe na shugaban kasar da na 'yan majalissun tarayya lafiya.
A bayanin da Mohammad Ibn Chmabas ya yi tun da farko, ya ce, kara karfin tsaro a duk fadin kasar ba ma kawai ya tafiyar da Boko Haram ba, har ma ya dakile yiwuwar tashin hankali na zabe da a kan yi a kasar, sai dai ya ce, rikicin Boko Haram ya yi kamari inda suka fara amfani da yara kanana suna kai harin kunar bakin wake, sannan kungiyar ta sanar da cewa, sun hade da kungiyar IS, domin tabbatar da cewa, jadawalinsu ya tsallaka Nigeriya.
Wakilin magatakardar MDD a yammacin Afrika Ibn Chambas daga nan ya yaba wa saurin daukin da kasashen yankin tabkin Chadi suka kawo musamman ta gudunmuwar sojojinsu, abin da ya kawo nasarar sake kwato yawan garuruwan da a baya kungiyar ta Boko Haram ta karbe a yankin arewa maso gabashin Nigeriya.
Ya yi bayanin cewa, a farkon wannan shekarar, kungiyar na rike da kananan hukumomi 20 a cikin jihohi 3 na yankin, amma a yanzu 'yan tsiraru ne kawai saboda sojojin gwamnati sun karbe a makon da ya gabata.
A bangaren jin kai kuwa, Madam Kang ta yi bayanin cewa, ayyukan kungiyar na Boko Haram sun tilasta wa mutane sama da miliyan 1.5 barin gidajensu a Nigeriya da kasashe makwabta.
A cewar Madam Kyung-wha Kang, kusan mutane miliyan 3 ne a arewa maso gabashin kasar ba za su iya samun abinci mai gina jiki ba, bayan watan Yulin bana, ban da matsalar tsaro, rashin samun agajin ma yana kawo karuwan masu bukatar jin kai. (Fatimah)