Magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi tir da kisan fararen hula da kungiyar Boko Haram ta yi a arewa maso gabashin Nigeriya. Ban Ki-moon ya yi wannann sukar ne sakamakon rahotannin da ya bayyana yawan mutanen da wannan kungiyar ta hallaka a harinta na baya bayan nan a garin Baga dake jihar Borno wanda ke kan iyaka da kasar Chadi a makon jiya.
Kamar yadda kakakin MDD ya bayyana, Mr. Ban har ila yau ya soki wannan harin na Maiduguri wanda aka yi amfani da yarinya 'yar shekara 10 aka dana mata bam din da ta tayar a tsakiyar kasuwa, abin da ya hallaka mutane a kalla 20 nan take.
Shugaban na MDD ya ce, majalisar a shirye take ta ba da agaji kowane iri ne da ya kamata ga gwamnatin Nigeriya, dama sauran kasashe makwabta wajen ganin sun shawo kan wannan matsalar ta tashe-tashen hankula da wahalhalun da al'umma suke fuskanta.
Kungiyar Boko Haram ta yi kaka gida a arewacin Nigeriya, tana ta tayar da bama bamai da kisan al'umma, abin da ya tilasta wa mazauna tserewa daga gidajensu zuwa sauran kasashen dake makwabtaka da su a yammacin Afrika.
Ofishin MDD a kan 'yan gudun hijira UNHCR ya bayyana cewa, hare-haren a jihar Borno ya tilasta wa mazauna kusan 7,300 tserewa zuwa yammacin kasar Chadi. (Fatimah)