in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga jami'an tsaro da su tabbatar da damke wadanda suka kai hari a Kenya
2014-07-07 10:10:43 cri

Mataimakin shugaban kasar Kenya Williams Ruto ya bukaci jami'an tsaro da su dukufa matuka, wajen ganin sun zakulo wadanda suka kaddamar da hare-haren baya bayan nan a yankunan dake gabar ruwan kasar. Rahotanni dai sun tabbatar da cewa, hare-haren biyu, da 'yan bindiga suka kaddamar da daren ranar Asabar sun hanlaka mutane 29.

Da yake jawabi ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su a garuruwan Mpeketoni da Hindi, Mr. Ruto ya ce, tuni ya baiwa manyan jami'an tsaron yankunan Nairobi da Lamu kwanaki biyu, da ko dai su gano wadanda suka kaddamar da hare-haren, ko kuma su shirya barin aikin su.

Hakan dai na zuwa ne bayan da rundunar 'yan sanda ta zargi kungiyar 'yan aware ta Mombasa ko MRC a takaice da laifin kitsa wannan hari, ko da yake dai tuni kungiyar Al-Shabaab ta ce ita ce ta kaddamar da hare-haren.

Bugu da kari, a yayin wata ganawa da ta yi da manema labarai a birnin Nairobi, mataimakiyar babban sifeton 'yan sanda yankin Grace Kaidi, ta ce, bayanan da suka tattara sakamakon binciken farko ya nuna cewa, 'yan kungiyar MRC ne suka aikata wannan mummunan aiki, bisa dalilai na siyasa da addini. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China