in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandan Kenya na neman mayakan Al-Shabaab bayan hari kan bas
2015-07-09 09:21:07 cri

Hukumomin kasar Kenya a ranar Laraban nan suka ce, yanzu haka ana neman 'yan kungiyar Al-Shabaab a garin dake bakin ruwa na Lamu saboda harin da suka kai a kan wassa motocin bas da yammacin ranar Talata.

Yan sandan sun ce, wadanda ake zargin mayakan Al-Shabaab ne sun yi kokarin kona wata motar 'yan sanda dake raka motocin bas dauke da fasinjoji daga Mombasa zuwa Lamu.

Kamar yadda wani babban jami'in 'yan sanda wanda ya nemi a sakaya sunan shi ya bayyana, an fara aikin binciken mayakan ne tun daga yammacin ranar Laraban. Ya ce, neman ya mika har cikin babban dajin Boni domin kamo mayakan da suka kai harin a kan motocin bas din guda 5 a kan hanyar Lamu zuwa Mombasa.

Rahotanni sun ce, mayakan sun fito ne daga daji, suka rika harbi kan mai uwa da wabi a kan motocin kafin 'yan sanda dake rakiyan motocin suka kore su.

Babu dai wanda ya ji rauni a harin da ya zo 'yan awanni kadan bayan da wani makamancin shi ya faru a wajen hakar ma'adinai na Mandera dake kusa da kan iyaka da kasar Somaliya inda aka hallaka mutane 14 da safiyar ranar Talata. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China