in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya alkawarta daukar karin matakan dakile ayyukan ta'addanci
2014-11-03 10:05:10 cri

Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya, ya sha alwashin kakkabe ayyukan ta'addanci daga daukacin sassan kasarsa.

Shugaban na Kenya ya bayyana hakan ne sakamakon aukuwar wasu hare-hare, da suka haddasa kisan 'yan sanda da dama a gundumar Turkana dake arewa maso yammacin kasar.

Yayin da yake jawabi bayan ziyarar da ya kai kauyukan Chesitet da Kapedo masu iyaka da gundumomin Baringo da Turkana, Kenyatta ya bukaci al'ummun yankunan da su mika dukkanin makaman da suka mallaka ba tare da izini ba ga jami'an tsaro. Ya ce, gwamnatinsa ba za ta lamunci daukar duk wani mataki da ka iya zama barazana ga rayukan fararen hula ba.

A daren Juma'ar da ta gabata ne dai wasu mahara suka afkawa yankin Kapedo, lamarin da ya haddasa kisan 'yan sanda 19, da wasu fararen hula 3, baya ga asarar dukiyoyi da tashin hankalin ya haifar.

Kafin wannan hari na ranar Juma'a ma dai, sai da wasu maharan sun kaddamar da farmaki kan wasu motocin 'yan sandan dake lura da majalissar dokokin kasar a ranar 22 ga watan Oktobar da ya shude, harin da shi ma ya haddasa kisan mutane 5, ciki hadda 'yan sanda 3.

Har wa yau a ranar 20 ga watan na Oktoba, an jikkata wasu 'yan sanda biyu, wadanda ke rakiyar wata mota mai dauke da takardun jarrabawar dalibai a Kapedo, kana maharan sun kone motar, tare da takardun da take dauke da su.

Shugaban kasar ta Kenya dai ya bayyana matukar takaicinsa ga yawaitar kisan 'yan sanda a kasar, yana mai cewa, zuwansa yankin da wannan lamari ya auku, na nuni ga muhimmancin da yake baiwa harkar tsaron kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China