in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyya mai mulki a Ghana ta ayyana shugaba Mahama a matsayin 'dan takararta a zaben 2016
2015-11-24 10:25:21 cri

A karshen wannan mako ne shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, ya karbi bukatar da jam'iyyar sa, wacce ke mulkin kasar wato National Democratic Congress (NDC) ta gabatar masa na nema ya sake tsayawa takara a zaben shugaban kasar na shekarar 2016.

Sakamakon kuri'un da aka kada ya nuna cewar, shugaba Mahama ya samu kashi 95 cikin 100 na amincewa a kan ya sake fitowa takarar a babban zaben kasar na badi.

Duk da cewa babu wanda ya nuna sha'awar tsayawa takarar shugabancin kasar a jam'iyyar, amma kundin tsarin mulkin jam'iyyar, ya nuna cewar, duk wanda aka gabatar da shi a matsayin 'dan takararta, dole ne ya samu a kalla kashi 50 cikin 100 na goyon bayan al'umma a zaben fidda gwani.

An dai gudanar da zaben fidda gwanin ne ta hanyar yin kuri'ar jin ra'ayin jama'a.

A jawabinsa na amincewa da matakin ba shi takarar, Mahama ya ce, zaben fidda gwanin zai ba da damar gudanar da yakin neman zaben cikin kwanciyar hankali, sannan ya ba da tabbacin yin aiki tukuru don ciyar da kasar gaba.(Ahmed Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China