Bisa labarin da aka bayar, an ce, a shekarar 2015, matsakaicin saurin bunkasuwar tattalin arziki na mambobin kasashe 6 na kungiyar ECCAS ya kai kashi 2.8 cikin 100, yayin da wannan adadi na shekarar 2014 ya kai kashi 4.8 cikin 100, an samu raguwa sosai.
Babbar hujjar da aka samu game da raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki a yankin shi ne, sakamakon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya daga watan Yuni na shekarar 2014, da matsalar tsaro da ke ci gaba da tsananta a wannan yanki. Bisa hasashen da kwamitin tsara manufofi ya yi, a shekarar 2016, matsakaicin karuwar tattalin arziki na mambobin kasashe na kungiyar zai ragu zuwa kashi 2 cikin 100.(Bako)