in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram 42
2016-07-22 10:39:40 cri

A kalla mayakan kungiyar Boko Haram 42 ne rundunar sojin Najeriya ta kashe a lokacin wani samame da ta kai a kauyen Garere dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar sojin kasar kanal Sani Usman da aka gabatarwa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, ya ce, kimanin mutane 80 wadanda aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da mata 38 da kananan yara 42 ne aka ceto da yammacin ranar Talatar.

Ya ce, an kai samamen ne bayan samun bayanan sirri da rundunar ta yi na taruwar mayakan na Boko Haram a yankin.

Usman ya ce, bayanan sirrin sun nuna cewar, mayakan na shirye shiryen kaddamar da hare hare kan al'ummomi mazauna yankunan.

Ya ce, tuni aka kwashe matan da kananan yaran da aka ceto zuwa asibitin sojoji dake Baga domin a bincika lafiyarsu.

Ya kara da cewar, rundunar sojin za su ci gaba da gudanar da sintiri a yankunan domin murkushe 'yan ta'adda dake addabar jama'a.

A wani ci gaban kuma, Usman ya ce, rundunar sojin ta yi nasarar damke mutumin da ake zargi da samarwa mayakan Boko Haram man fetur a jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin ya ce, an kama mutumin ne a wajen binciken ababan hawa na Molai dake wajen birnin Maiduguri da misalin karfe 8 na safiyar ranar Talatar.

Usman ya ce, a binciken da suka gudanar sun gano cewa, mutumin ya jima yana wannan sana'ar inda yake samarwa mayakan Boko Haram man fetur da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum a dajin Sambisa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China