in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar Najeriya ta iso Beijing domin tattauna makomar taron FOCAC
2016-07-26 09:08:39 cri

Ministan ma'aikatar kasafin kudi da tsare tsare a tarayyar Najeriya Udoma Udo Udoma, ya jagoranci tawagar gwamnatin Najeriya zuwa nan birnin Beijing na kasar Sin, domin halartar taron duba makomar shawarwarin da aka gudanar a baya, tsakanin kasar ta Sin da kasashen Afirka karkashin dandalin FOCAC.

Kaza lika tawagar za ta nazarci ci gaban da aka samu, tare da karfafa manufar aiwatar da yarjeniyoyin da aka cimma, tsakanin gwamnatin kasar Sin da Najeriya, yayin ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ya gudanar a nan kasar Sin cikin 'yan watannin baya.

Wata sanarwa da gwamnatin Najeriyar ta fitar, ta ce, an dorawa wannan tawaga nauyi na tabbatar da Najeriyar ta shiga an dama da ita, a muhimman fannoni 10 da suka shafi hadin gwiwar sassan biyu. Fannonin dai sun kunshi bunkasa noma a zamanance, da samar da ababen more rayuwa, da raya masana'antu, da amfani da makamashi mai tsafta, da kuma hadin gwiwa a fannin hada hadar kudi.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China