NNS UNITY, wani jirgin ruwan yaki na sintiri na rundunar sojojin ruwan Najeriya, da aka saya daga kasar Sin, ya isa kasar Afrika ta Kudu a ranar Litinin.
NNS UNITY shi ne jirgin ruwan yaki na biyu da Najeriya ta saya daga kasar Sin, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa domin hadewa da sauran jiragen ruwan yakin Najeriya.
Wannan jirgin ruwan yaki zai taimaka sosai wajen kara karfi da mayar da martani yadda ya kamata game da kalubalolin tsaro a cikin ruwan Najeriya, a cewar jami'an Najeriya.
Abolade Ogunlege, wani babban hafsan jirgin ruwan yakin NNS UNITY, ya bayyana cewa, wannan jirgin ruwan yaki zai tallafawa kokarin yaki da manyan laifuffukan teku da wasu ayyukan keta doka kan ruwan Najeriya da kuma tekun Guinea baki daya. (Maman Ada)