in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar matasan Afrika ta bukaci a samar da asusun tallafawa matasan Burundi
2016-06-27 09:36:06 cri

Shugabar kungiyar matasan kasashen Afrika Francine Muyumba ta bukaci shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza da ya samar da wani asusu don tallafawa matasan kasar ta Burundi, Muyumba ta yi wannan kira ne bayan da ta yi ganawa da shugaban kasar a lardin Makamba a ranar Asabar da ta gabata.

Shugaba Nkurunziza ya gana da Muyumba ne a yayin da ya kai ziyarar kaddamar da wasu ayyukan ci gaban yankin na Makamba, wanda ke da tazarar kilomita 200 daga babban birnin kasar Bujumbura.

Muyumba ta ce, sun tattauna da shugaban kasar batutuwa da suka shafi zuba jari domin matasa su ci moriyarsu. Sannan ta ce, sun tattauna ka'idar matasan Afirka, wadda ake sa ran za ta samu amincewa daga dukkan kasashe mambobin kungiyar tarayyar Afrika, kafin karshen wannan shekara, kuma a cewarta shugaban kasar ya amince da bukatun nasu.

Sannan ta ce, ta gabatar da bukata ga shugaban kasar na kafa wata gidauniya don ci gaban matasan kasar wadda za ta dinga samar da rancen kudade don matasan Burundi su samu sana'o'in dogaro da kansu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China