in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyya mai mulki a Burundi za ta zabi sabbin shugabanni nan da watanni 2
2016-06-20 09:44:14 cri

Jam'iyyar CNDD-FDD mai mulki a kasar Burundi za ta zabi shugabanninta cikin watanni biyu, jam'iyyar ce ta sanar da hakan a Lahadin da ta gabata bayan kammala babban taronta.

An gudanar da mashahurin taron ne tsawon kwanaki biyu a garin Ngozi, mai tazarar kilomita 125 dake arewacin Bujumbura, babban birnin kasar.

Pascal Nyabenda, shugaban jam'iyya mai mulkin Burundi ya bayyana cewar, sun kammala taron cikin nasara, kuma babban abin da taron ya maida hankali shi ne gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin jam'iyyar da dokokinta, domin jam'iyyar ta kara karfi da samun karbuwa a wajen dimbin magoya baya.

Nyabenda ya ce, sun aiwatar da sauye sauye masu yawa game da tsarin gudanarwar jam'iyyar. Sannan ya ce, za su gabatar da sabbin sauye sauyen ga ma'aikatar al'amurran cikin gidan kasar domin amincewa da su.

Mai magana da yawun jam'iyyar ta CNDD-FDD Daniel Gelase Ndabirabe ya ce, za'a sauya shugabannin dake jan ragamar jam'iyyar a halin yanzu cikin watanni biyu.

Shugaba Pierre Nkurunziza, na kasar wanda ya samu halartar gangamin, ya bayyana cewar, jam'iyyar mai mulki tana sake yin karfi fiye da a lokutan baya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China