Kwamishinan 'yan sanda na kasar Burkina Faso Lazare Tarpaga ya ce, jami'ansa sun yi nasarar kashe wani da ake zaton mai kishin jihadi ne, yayin wani samame da suka kaddamar a cibiyarsu da ke yankin arewa maso yammacin wajen birnin Ouagadougou, babban birnin kasar da nufin tarwatsu.
A cikin wata sanarwa da 'yan sandan suka rabawa manema labarai, sun bayyana cewa, mutumin yana rike da wata karamar bindiga da kuma wani abin fashewa a lokacin da suka harbe shi a musayar wutar da suka yi.
Hukumomin tsaro sun bayyana cewa, 'yan sandan sun kuma yi nasarar kama wasu daga cikin masu ra'ayin jihadin, sai dai kuma ba a bayyana adadin mutanen da aka kama ba. Yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da bincike.
A cewar kwamishinan 'yan sandan, 'yan ta'addan suna kokarin daukar matasa ne domin su shigar da su kungiyarsu.
A 'yan shekarun da suka gabata dai kasar Burkina Faso tana fama da hare-haren ta'addanci da yunkurin juyin mulki daga rukunin sojoji na musamnan da ke gadin fadar tsohon shugaban kasar Blaise Compaore. (Ibrahim)