in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burkina-Faso ta bayyana jinkirtawa game da batun janyewar AU daga kotun ICC
2016-07-20 11:08:20 cri

Kasar Burkina-Faso ta bayyana jinkirtawa game da batun janyewar kungiyar tarayyar Afrika (AU) daga kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya (ICC) da wasu masanan Afrika suke adawa da yadda take gudanar da aikinta, in ji shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, bayan da ya dawo daga birnin Kigali na kasar Rwanda, inda ya halarci taron kolin kungiyar AU karo na 27.

Burkina Faso tare da wasu kasashen Afrika guda shida, sun bayyana jinkirtawa, sai an yi la'akari da dokokin ko wace kasa, domin ba da damar yin shawarwari kan amincewa ko a'a da wannan mataki, in ji mista Kabore bayan saukarsa daga jirgin sama a Ouagadougou.

Ya nuna cewa, za su mai da hankali kan wannan muhimmin batu, domin tarayyar Afrika na ganin cewa, kotun Afrika na da karfi da kwarewa wajen gurfanar da shugabannin kasa.

Kotun ICC, wata kotu ce ta din din din dake da hurumin yi wa mutanen da ake zargi da kisan kare dangi, manyan laifuffukan cin zarafin dan adam, laifuffukan yaki da sauransu. A wannan lokaci, masana da dama, musammun ma 'yan Afrika na kiran kasashensu da su janye daga kotun da suke zargi na da nacewa kan gurfanar da shugabannin Afrika kawai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China