in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke mutane 10 da ake zargi da kai harin ta'addanci a Burkina Faso
2016-07-01 09:44:20 cri

Yan sandan kasar Burkina Faso sun cafke wasu mutane goma, da suka hada mutane uku da aka zarginsu sosai, kana kuma suna neman wasu sauran mutane shida, yayin da suke binciken harin ta'addancin ranar 15 ga watan Janairun shekarar 2016 a birnin Ouagadougou, da kuma harin ranar 13 ga watan Maris a Grand Bassam, wani birnin kasar Cote d'Ivoire, in ji ministan tsaron cikin gidan Burkina Faso, Simon Campaore a ranar Alhamis.

Haka kuma, wasu 'yan kasar Burkina Fason biyu da suka bukaci a kafa wata kungiyar 'yan ta'adda a kasar su ma ana tsare su tun a shekarar 2015, in ji ministan.

Sun samu horo a kasar Nijar, kuma sun halarci kai hare haren ta'addanci da dama a kasar Mali, musammun ma kan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar ta Mali, in ji mista Campaore. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China