in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun ICC ta tuhumi tsohon mataimakin shugaban DRC Bemba
2016-03-22 10:41:15 cri

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa dake Haque ta sanar a ranar Litinin cewa, tana tuhumar tsohon mataimakin shugaban kasar jamhuriyar demokradiyar Kongo DRC Jean-Pierre Bemba Gombo da aikata manyan laifuka yaki da cin zarafin bil adama.

A matsayin babban jagoran kungiyar MLC ta Kongo, Bemba ya dauki dakarun kungiyar 1500 zuwa jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR a shekara ta 2002 bisa ga bukata da kuma neman gudunmuwa da tsohon shugaban kasar Ange-Felix Patasse ya yi.

Kotun ta rigaya ta gano cewar, a lokacin da aka yi tashin hankali tsakanin watan Oktoban shekara ta 2002 zuwa watan Maris din 2003, dakarun kungiyar ta MLC bisa sanin su da kuma niyya sun aikata laifuffuka da dama da suka hada da tsokanan fada, fyade, da kuma kisan kai a wurare da dama a kasar ta jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Kotun ta tabbatar da zargin cewa, Bemba ya yi amfani da cikakken ikon shi a kan dakarun shi na MLC, kuma da sanin shi dakarun suka aiwatar da wannan laifukan ko suka yi niyyar aiwatarwa, kamar yadda mai shari'a Sylvia Steiner daga kasar Brazil ta gabatar.

An fara zaman sauraron shari'ar ta Bemba tun daga ranar 22 ga watan Nuwamba na shekara ta 2010, kuma an gama karban bayanan shaidu a ranar 7 ga watan Afrilun shekara ta 2014.

Bemba dai ya musunta duk zargin da ake mashi.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China