in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Rwanda sun kutsa kai a DRC wajen neman 'yan tawayen FDLR
2016-04-20 10:52:39 cri

Hukumomin jamhuriyar demokaradiyyar Congo DRC sun tabbatar a ranar Talata cewa, sojojin Rwanda sun kutsa kai a yayin da suke neman 'yan tawayen FDLR a wani yankin na kasar.

"Ko shakka babu, rundunar Rwanda ta shigo cikin kasar Congo", in ji kaftan Guillaue Ndjike Kaiko, darektan sadarwa na rundunar sojojin FARDC na yanki na 34, a yayin wani taron manema labarai a birnin Goma.

Kaftan Guillaue Ndjike Kaiko, ya yi wannan sanarwa a lokacin da yake gabatarwa 'yan jarida sakamakon binciken da tawagar rundunar ta yi a yankunan. Wannan tawaga, an dora mata nauyin yin bincike da samar da bayanai daga wajen al'umma da kuma shugabanninsu kan wadannan korafe korafe na shigowar sojojin kasar Rwanda a cikin kasar Congo.

Wannan sakamakon bincike ya yi bayani kan daruruwan sojojin rundunar kasar Rwanda da suka shigo cikin kasar Congo ta hanyar layin kan iyaka mai lamba 123 a ranar Asabar 16 ga watan Afrilun da ya gabata, a cewar wasu shaidun da aka samu daga wajen al'ummomi dake wannan wuri. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China