Kungiyar ta OPEC, ta kuduri aniyar tattauna muhimman batutuwa da suka shafi takaita hako danyen mai a tsakanin kasashen da basa cikin kungiyar ta OPEC, ciki harda Rasha a watan Nuwamba.
Kafafen yada labaru sun rawaito Muhammad Barkindo, sakatare janar na OPEC a jiya Talata na cewa, ya yi watsi da duk wani shakku da ake da shi kan kasar Rasha, game da kin amincewa da shirin takaita hako danyen man, yana mai cewa, kasar Rasha tana yin namijin kokari wajen ganin farashin danyen man ya daidaita a kasuwannin duniya.
A makonni 3 da suka gabata, farashin danyen man ya karu da kashi 13 cikin 100, bayan da OPEC ta fitar da matakan takaita hako albarkatun man irinsa na farko cikin shekaru 8.(Ahmad Fagam)