Kungiyar wadda ta bayyana hakan cikin wani rahoto da ta fitar a jiya Laraba ta ce, za ta ci gaba da hako danyen mai, duk da faduwar farashinsa a kasuwannin duniya.
Rahoton kungiyar ya kuma nuna cewa, ana ci gaba da hako danyen mai ne galibi a kasashe kamar su Najeriya, Iraki, Saudiyya da kuma Iran wadda ta ce za ta kara yawan man da ke hakowa jim kadan bayan cire mata takunkumin da aka kakaba mata.
Bayanai na nuna cewa, da alamun kasashe mambobin kungiyar ba za su rage yawan man da suke hakowa ba ta yadda zai yi dai-dai da bukatun kasuwanni. Wannan ya sa kungiyar ke ci gaba da hako sama da ganga miliyan 30 na danyen mai a kowa ce rana. (Ibrahim)