in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar OPEC ba ta cimma daidaito game da yawan man fetur da za a samar ba
2016-06-03 11:16:12 cri
Bayan da mambobin kungiyar kasashe masu samar da man fetur wato OPEC suka shafe sa'oi 4 suna shawrawari a jiya Alhamis, kasashen ba su cimma daidaito game da yawan man fetur din da za a hako ba.

A jiyan ne kungiyar ta OPEC ta shirya taro karo na 169 a birnin Vienna dake kasar Austria game da yawan man fetur din da za a hako, kuma wannan shi ne karo na 2 da kungiyar ta kasa cimma daidaito game da yawan man fetur din da za a hako. Yanzu, kungiyar na hako man fetur da yawansu ya kai ganguna miliyan 32 a ko wace rana, a baya, an tsaida cewa, za a hako ganguna miliyan 30 ne a ko wace rana.

Rahotanni na cewa, makasudin shirya taron shi ne, a tsara wani sabon shiri game da yawan man da ya kamata a rika hako wa, don biya bukatun yanayin da ake ciki yanzu, duk da cewa, kasashe mahalartar taron suna da rarrabuwar kawuna, inda kowace kasa ta dage kan yawan man da take son hakowa

Tun daga farkon shekarar bana, farashin man fetur ya fadi a kasuwannin duniya. Amma daga watan Maris, farashin ya dan tashi, ganin haka ya sa kungiyar OPEC ta bayyana a sanarwar bayan taron nata cewa, za a daidaita kasuwannin man fetur yadda ya kamata.

Kungiyar OPEC ta sanar da cewa, za a yi taro mai zuwa a ranar 30 ga watan Nuwambar bana a birnin Vienna.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China