in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
OPEC: Farashin gangan man fetur zai sake tashi zuwa dala 70 a shekarar 2020
2015-12-28 10:57:05 cri

Jaridar Arab News ta kasar Saudiyya ta ruwaito kamfanin dillancin labarai na AFP yana cewa, kungiyar kasashen da ke hako man fetur ta OPEC ta yi hasashen cewa, sakamakon karuwar bukatun man fetur daga kasashen duniya, da kuma yadda kasashen da ba kungiyar OPEC ba ba su iya samar da man fetur kamar aka yi hasashe, yanayin da kasuwar man fetur ke ciki zai samu kyautatuwa. Ban da haka, bisa rahoton shekara-shekara da OPEC ta fitar kan makomar man fetur a duniya, an kiyasta cewa, farashin gangan man fetur zai kai dala 70.7 a shekarar 2020, sannan zai tashi zuwa dala 95 a shekarar 2040.

Rahoton ya kara da cewa, ganin yadda OPEC ta yi watsi da manufar kayyade farashin man fetur ta hanyar rage yawan man da ake hakowa, da kuma aiwatar da manufar korar kamfanonin Amurka da ke hako mai daga dutsawu don kayyade yawan kason da kungiyar ta samu a kasuwar duniya, farashin man fetur ya ragu da kashi 60 cikin dari a cikin shekara daya da rabin da suka gabata.

Bugu da kari, rahoton ya ce, yawan bukatun danyen mai a duniya zai kai ganga miliyan 974 a kowace rana a shekarar 2020. Ko da yake man da OPEC za ta bukata zai karu bisa hasashen da aka yi a cikin shekaru biyar masu zuwa, amma adadin ba zai kai na yanzu ba. Haka zakila, kungiyar ta ce, ya zuwa shekarar 2040, yawan kason da kungiyar za ta samu a duniya zai karu zuwa kashi 37 cikin dari. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China