in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin kamfanin Air China ya fara safara zuwa Habasha
2015-11-03 10:18:08 cri

A jiya ne jirgin saman kamfanin Air China, daya daga cikin manyan jiragen saman kasar ya fara safara daga Beijing zuwa Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. Kasa ta biyu a Afirka da jiragen kamfanin suka fara zirga-zirga a halin yanzu, bayan Afirka ta Kudu.

Babban jami'in kamfanin jiragen sama na kasar Habasha Tewolde Gebremariam, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua yayin bikin kaddamar da jirgin cewa, matakin zai bunkasa hadin gwiwa da abokanta tsakanin kasar Habasha da kamfanin Air China.

Shi ma babban mataimakin shugaban kamfanin jiragen sama na Air China Liu Tiexiang, ya bayyana cewa, kaddamar da hanyar za ta kara baiwa kamfanonin Sin damar kara zuba jari a nahiyar Afirka baya ga saukaka zirga-zirga tsakanin Sin da Afirka.

Jami'ai da ma'aikatan hukumar kula da filayen jiragen sama na kasar Habasha da na kamfanonin jiragen sama na Habasha da Air China da wasu jami'an diplomasiya da ke kasar ta Habasha ne suka tarbi jirgin na Air China samfurin Air Bus A330 a lokacin da ya sauka a filin jiragen sama na Bole da ke Addis Ababa.

Birnin na Addis Ababa dai na zama hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka ta AU da ta hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka (UNECA) da sauran kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China