in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Habasha sun jaddada burin hada kai da juna a dukkanin fannoni
2015-04-10 10:50:43 cri

Kasashen Sin da Habasha sun bayyana burinsu na fadada matsayin dangantakarsu a dukkanin fannonin ci gaba.

Hakan na kunshe, cikin jawabin da wakilan sassan biyu suka gabatar, a yayin bikin maraba da zuwan sabon jakadan Sin a kasar Habasha La Yifan. Wakilan kasashen biyu dai sun bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ta hada da ta bangaren gwamnati da gwamnati, da ta jam'iyyun kasashen biyu, da kuma dangantakar 'yan kasuwar sassan biyu.

Da yake tsokaci gaban mahalarta taron marabar, Mr. La wanda shi ne jakadan Sin na 13 a kasar Habasha, ya ce, tun bayan kulla dangantakar kasashen biyu shekaru 45 da suka gabata, Sin ke ci gaba da karfafa hulda tsakaninta da daukacin kasashen Afirka, da ma ita kanta kasar ta Habasha.

La Yifan ya kara da cewa, a halin yanzu kasarsa na da burin bunkasa hadin gwiwa da Habasha, ta yadda sassan biyu za su ci gaba da cin moriyar juna, tare da cimma manufofinsu na wadata.

Ya ce, kasashen biyu na da babban zarafi na samun ci gaba a fannin tattalin arziki, matakin da ka iya bude kofofin habaka masana'antu, sashen da Sin ke matukar fatan taimakawa Habasha cimma gajiyarsa.

Har wa yau, ya bayyana aniyar kasar Sin ta taimakawa Habashan wajen warware matsalolinta na sufuri, da na yaki da talauci.

A nasa bangare, ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Habasha Berhane Gebre-Christos, cewa ya yi, kasarsa za ta ci gaba da karfafa huldarta da Sin a dukkanin fannoni.

Berhane ya ce, Sin na tallafawa Habasha wajen yaki da fatara, da kuma cimma muradun tattalin arziki.

A cewarsa, Habasha ta tsara kudurorin bunkasuwar tattalin arziki da take fatan aiwatarwa nan da shekarar 2025, za kuma ta fidda manufofin samar da sauyi kashi na biyu wadda aka yiwa lakabi da GTP-2, bayan da ta cimma nasarar kashi na farko na kudurorin cikin shekaru 5. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China