in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da farar takarda game da ci gaban da kasar ta samu a fannin kare hakkin bil-Adama bisa doka
2016-09-12 11:07:43 cri

A yau ne ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wata farar takarda wadda ke bayani dalla-dalla game da sabbin ci gaba da mahukuntan kasar suka samu a fannin kare hakkin bil-adama bisa doka.

Farar takardar wadda aka yi mata lakabi da "Sabon ci gaba da aka samu a kasar Sin a fannin kare hakkin bil-Adama bisa doka" ta bayyana cewa, bangaren shari'a shi ne mataki na karshe na kare hakkin jama'a da nuna adalci. Kuma kare hakkin bil-Adama bisa doka, wani bangare ne mai matukar muhimmanci ga ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kare hakkin bil-Adama.

Takardar ta kuma bayyana cewa, a 'yan shekarun nan, musamman tun lokacin da aka gudanar da babban taron JKS karo na 18, an samu gagarumin ci gaba wajen zamanantar da tsarin shari'a da karfin tafiyar da harkokin mulkin kasa.

Bugu da kari, mahukuntan kasar sun taka muhimmiyar rawa wajen kare hakki da 'yancin jama'a a fannoni daban-daban kamar yadda doka ta tanada, yayin da su ma jama'a suka sauke nauyin da ke kansu yadda ya kamata.

Sai dai kuma, duk da irin ci gaban da aka samu, takardar ta ce, za a ci gaba da daukar matakan da suka wajaba na karfafa dokokin da suka shafi kare hakkin bil-Adama, haka kuma mahukuntan kasar za su dora kan ci gaban da aka samu, koyi da nasarorin da wasu kasashe suka samu ta hanyar tafiyar da mulki bisa doka, kare hakkin bil-Adama kamar yadda doka ta shafa, kare jin dadin jama'a da nuna adalci, da kuma aiwatar da doka a dukkan fannoni.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China