in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An hukunta wadanda suka aikata laifuka masu nasaba da yanar gizo da wayoyin tarho
2016-10-18 10:46:12 cri

Mahukuntan kasar Sin sun hukunta mutane da yawan su ya kai 43,000, bayan da aka tabbatar sun aikata laifuka masu alaka da zamba ta kafofin wayar tarho da kuma yanar gizo. Rundunar 'yan sandan kasar ta ce an kammala hukunce hukunce 77,000 masu alaka da wadannan laifuka, tsakanin watan Janairu zuwa Satumbar wannan shekara.

Yayin wani taron manema labarai da ma'aikatar tsaron jama'a ta kasar Sin ta shirya a ranar Litinin, an bayyana cewa, a bana laifukan da aka aikata ta yanar gizo da kafofin wayar tarho, sun karu da ninki 2.3, idan an kwatanta da na shekarar bara.

Kaza lika 'yan sanda sun rufe wasu dakunan sirri da ake boye haramtattun kayayyaki da kudaden haram, wadanda darajar su ta kai dalar Amurka miliyan 347. Jami'an tsaro sun tabbatar da cewa, daukar wannan mataki ya kare al'umma daga asarar da ka iya kaiwa ta kudin Sin Yuan biliyan 4.75.

Da yake karin haske game da hakan, mataimakin ministan ma'aikatar tsaron jama'a Li Wei, ya ce ma'aikatar sa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin ta na baiwa al'umma kariya, tare da tallafawa wadanda aka damfasa damar karbar dukiyoyin su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China