in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na shirin harba na'urar bincike zuwa Mars nan da shekarar 2020
2016-08-24 10:44:32 cri

A jiya Talata kasar Sin ta nuna wasu hotuna dake tabbatar da aniyarta ta harba na'urar bincike zuwa duniyar Mars cikin shekaru 5.

Zhang Rongqiao, shi ne babban jami'i mai lura da al'amurran da suka shafi duniyar Mars, ya fada a taron manema labaru a Beijing cewa, kasar Sin tana shirye shiryen harba na'urar zuwa Mars, wanda take sa ran za ta isa duniyar a watan Yuli ko Agusta na 2020. Ya ce, ana fuskantar babban kalubale ne.

A cewar Ye Peijian, daya daga cikin masanan harkokin 'yan sama jannati, kuma kwararre a wannan fanni, za'a kaddamar da wannan shirin na 2020 ne ta hanyar amfani da roka ta Changzheng-5 daga cibiyar harba kumbon dake Wenchang a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China