in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da nacewa manufofi biyu na warware batun tekun kudanci
2016-07-25 09:43:55 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, kasar sa za ta ci gaba da nacewa manufofin nan biyu, wajen warware batun tekun kudancin kasar. A cewar Mr. Wang, manufofin sun kunshi gudanar da shawarwari kai tsaye da masu ruwa da tsaki, tare da amfani da inuwar kungiyar hadin kan kasashen kudu maso gabashin Asiya (ASEAN), wajen tabbatar da zaman lafiya da lumana, a yankunan kudancin tekun na Sin da ake takaddama a kan su.

Minista Wang dai na wannan tsokaci ne yayin ganawar sa da minista na biyu a ma'aikatar harkokin waje da cinikayyar kasar Brunei Lim Jock Seng a ranar Asabar, gabanin taron kungiyar (ASEAN) da aka bude a birnin Vientiane na kasar Lao.

Ya kara da cewa, bisa irin kyakkyawar alakar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasahen dake kungiyar ta ASEAN, Sin da Brunei na da matsaya guda, game da aniyar warware matsalar tekun na kudancin Sin cikin lumana.

Mr. Wang na ganin manufofin da Sin ta amince da su sun dace da dokokin da aka amincewa, game da mu'amalar kasashen yankin tekun na kudancin Sin ko (DOC) a takaice, da ma dokokin MDD wadanda suka shafi hurumin kasashe daban daban.

A nasa bangare, Mr. Lim Jock Seng, cewa ya yi, Brunei ta dade tana marawa wadannan manufofi na kasar Sin baya. Kaza lika ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar ASEAN da ita kan ta kasar Sin, da su tabbatar da cimma nasarar aiwatar da dokokin DOC da aka amince da su, yayin da kuma suke ci gaba da tattaunawa kan tsarin gudanarwa a tekun kudancin Sin, matakan da a cewar sa, su ne za su tabbatar da zaman lafiya da tsaro a wannan yanki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China